Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 19:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya amsa.

2. “Me ya sa kuke azabta ni da maganganu?

3. A kowane lokaci kuna wulakanta ni,Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina.

4. Da a ce ma na aikata abin da yake ba daidai ba ne,Da me ya cuce ku?

5. Tsammani kuke kun fi ni ne,Kuna ɗauka cewa wahalar da nake shaTa tabbatar ni mai laifi ne.

6. Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini,Ya kafa tarko don ya kama ni.

7. Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba,Amma ba wanda ya kasa kunne.Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.

8. Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa,Ya rufe hanyata da duhu,

9. Gama ya kwashe dukiyata duka,Ya ɓata mini suna.

10. Ya mammangare ni,Ya tumɓuke sa zuciyata,Ya bar ni in yi yaushi, in mutu.

11. Allah ya zaburo mini da fushi,Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.

12. Ya aiko da rundunar sojansa don ta fāɗa mini,Suka haƙa ramummuka kewaye da alfarwata inda za su yi kwanto.

13. “'Yan'uwana sun yashe ni,Na zama baƙo ga idon sanina.

14. Dangina da abokaina sun tafi.

Karanta cikakken babi Ayu 19