Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 18:8-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Yana tafiya, sai ya fāɗa cikin tarko.Tarkon ya kama ƙafafunsa.

9. Tarko ya kama diddigensa ya riƙe shi,

10. An binne masa tarko a ƙasa,An kafa masa tarko a hanyarsa.

11. “Kewaye da shi duka razana tana jiransa,Duk inda ya nufa tana biye da shi,

12. Dā attajiri ne, amma yanzu ya talauce,Kusa da shi bala'i na tsaye yana jiransa.

13. Mummunan ciwo ya bazu ko'ina a jikinsa,Yana sa hannuwansa da ƙafafunsa su ruɓe,

14. Dā yana zaune lafiya,Sai razana ta tatike shi,Ta jawo shi zuwa ga Sarkin Mutuwa.

15. Yanzu kowa zai iya zama a alfarwarsa,Bayan da an karkashe ƙwayoyin cuta da farar wuta.

16. Saiwoyinsa da rassansa suka yi yaushi suka bushe.

17. Sunansa ya ƙare a gida da a jeji,Ba wanda yake ƙara tunawa da shi.

18. Za a kore shi daga ƙasar masu rai,Za a kore shi daga haske zuwa duhu.

19. Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.

20. Daga gabas zuwa yamma, duk wanda ya ji labarin ƙaddarar da ta same shi,Zai yi makyarkyata, ya yi rawar jiki don tsoro.

21. Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,Wannan ita ce ƙaddarar mutane waɗanda ba su damu da kome na Allah ba.”

Karanta cikakken babi Ayu 18