Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 17:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ƙarshen raina ya gabato, da ƙyar nake numfashi,Ba abin da ya rage mini sai kabari.

2. Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba'a.

3. Ni amintacce ne, ya Allah, ka yarda da maganata.Ba wanda zai goyi bayan abin da nake faɗa.

4. Ka baƙantar da hankalinsu, ya Allah,Kada ka bar su su yi mini duban wulakanci yanzu.

5. A karin maganar mutanen dā an ce,‘Kowa ya ci amanar abokinsa saboda kuɗi,'Ya'yansa sā sha wahala!’

6. Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.Da mutane suka ji,Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.

Karanta cikakken babi Ayu 17