Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 15:5-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu,Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.

6. Ba na bukata in kā da kai,Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.

7. “Kana tsammani kai ne mutumin da aka haifa na farko?Sa'ad da Allah ya yi duwatsu kana nan?

8. Ko ka taɓa jin shirye-shiryen da Allah ya yi?Ko kai kaɗai kake da hikima a cikin mutane?

9. Ba wani abu da ka sani da mu ba mu sani ba.

10. Daga wurin mutanen da suka yi furfura muka koyi hikimarmu.Mun koyi hikimarmu daga mutane waɗanda aka haife suTun kafin a haifi mahaifinka.

11. “Allah yana ta'azantar da kai,Me ya sa har yanzu ka ƙi kulawa da shi?Mun yi magana a madadinsa a natse da lafazi mai daɗi.

12. Amma ka ta da hankalinka,Kana ta zazzare mana ido da fushi.

13. Fushi kake yi da Allah, kana ƙinsa.

14. Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai?Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah?

15. Me ya sa Allah bai sakar wa mala'ikunsa kome ba?Har su ma ba tsarkaka suke a gare shi ba.

16. Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa,Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.

17. “Yanzu ka saurara, ya Ayuba, ga abin da na sani.

18. Mutane masu hikima sun koya mini gaskiyaWadda suka koya daga wurin kakanninsu,Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.

Karanta cikakken babi Ayu 15