Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 15:20-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. “Mugun mutum mai zaluntar sauran mutaneZai kasance da wahala muddin ransa.

21. Zai ji ƙarar muryoyi masu firgitarwa a kunnuwansa.'Yan fashi za su fāɗa masaSa'ad da yake tsammani ba abin da zai same shi.

22. Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba,Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.

23. Yana ta yawon neman abinci, yana ta cewa, ‘Ina yake?’Ya sani baƙin ciki ne yake jiransa a nan gaba. Kamar sarki mai iko,

24. Haka masifa take shirin fāɗa masa.

25. “Wannan shi ne ƙaddarar mutum,Wanda ya nuna wa Allah yatsa,Ya kuwa raina Mai Iko Dukka.

26. Wannan mutum mai girmankai ne, ɗan tawaye.

27. Ya ɗauki garkuwarsa kamar ɗan yaƙi,Ya ruga don ya yi yaƙi da Allah.

28. Shi ne mutumin da ya ci birane da yaƙi,Ya ƙwace gidajen waɗanda suka tsere,Amma yaƙi ne zai hallaka birane da gidaje.

29. Arzikinsa ba zai daɗe ba,Duk abin da ya mallaka ba zai daɗe ba.Har inuwarsa ma za ta shuɗe,

30. Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba.Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa,Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.

31. Idan wauta tasa ta kai shi ga dogara ga mugunta,To, mugunta ce kaɗai zai samu.

32. Kafin kwanakinsa su cika zai bushe,Zai bushe kamar reshe, ba zai ƙara yin ganye ba.

Karanta cikakken babi Ayu 15