Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 15:18-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Mutane masu hikima sun koya mini gaskiyaWadda suka koya daga wurin kakanninsu,Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.

19. Ƙasaru 'yantacciya ce daga baƙiBa wanda zai raba su da Allah.

20. “Mugun mutum mai zaluntar sauran mutaneZai kasance da wahala muddin ransa.

21. Zai ji ƙarar muryoyi masu firgitarwa a kunnuwansa.'Yan fashi za su fāɗa masaSa'ad da yake tsammani ba abin da zai same shi.

22. Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba,Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.

Karanta cikakken babi Ayu 15