Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 15:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Elifaz ya yi magana.

2. “Surutai, Ayuba! Surutai!

3. Ba wani mai hikima wanda zai yi magana irin taka,Ko kuma ya kāre kansa da irin maganganun da ba su da ma'ana.

4. Kana karya jama'a, kana hana su jin tsoron Allah,Kana hana su yin addu'a gare shi.

5. Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu,Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.

Karanta cikakken babi Ayu 15