Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 14:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare,Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.

8. Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa,Kututturensa kuma ya ruɓe a ƙasa,

9. In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.

10. Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan,Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?

11. “Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu,Har tekuna kuma su ƙafe.

12. Amma matattu ba za su tashi ba daɗai,Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan.Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.

13. “Ya Allah, da ma a ce ka ɓoye ni a lahira,Ka bar ni a ɓoye, har fushinka ya huce,Sa'an nan ka sa lokacin da za ka tuna da ni!

14. Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma?Amma zan jira lokaci mafi kyau,In jira sai lokacin wahala ya wuce.

15. Sa'an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa,Za ka yi murna da ni, ni talikinka.

Karanta cikakken babi Ayu 14