Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 14:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu,Har tekuna kuma su ƙafe.

12. Amma matattu ba za su tashi ba daɗai,Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan.Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.

13. “Ya Allah, da ma a ce ka ɓoye ni a lahira,Ka bar ni a ɓoye, har fushinka ya huce,Sa'an nan ka sa lokacin da za ka tuna da ni!

14. Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma?Amma zan jira lokaci mafi kyau,In jira sai lokacin wahala ya wuce.

15. Sa'an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa,Za ka yi murna da ni, ni talikinka.

16. Sa'an nan za ka lura da kowace takawataAmma ba za ka bi diddigin zunubaina ba.

Karanta cikakken babi Ayu 14