Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 14:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.

2. Sukan yi girma su bushe nan da nan kamar furanni,Sukan shuɗe kamar inuwa.

3. Na ma isa ka dube ni ne, ya Allah?Ko ka gabatar da ni a gabanka,Ka yi mini shari'a?

4. Ba wani abu tsarkakakkeDa zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.

5. Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can,An ƙayyade yawan watannin da zai yi,Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.

6. Ka kawar da fuska daga gare shi, ka rabu da shi,Ka bar shi ya ji daɗin kwanakinsa na fama da aiki idan zai iya.

7. “Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare,Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.

8. Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa,Kututturensa kuma ya ruɓe a ƙasa,

9. In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.

10. Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan,Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?

11. “Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu,Har tekuna kuma su ƙafe.

12. Amma matattu ba za su tashi ba daɗai,Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan.Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.

Karanta cikakken babi Ayu 14