Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 12:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Yakan mai da hikimar masu mulki wauta,Yakan mai da shugabanni marasa tunani.

18. Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.

19. Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.

20. Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su.Yakan kawar da hikimar tsofaffi.

21. Yakan kunyatar da masu iko,Ya hana wa masu mulki ƙarfi.

22. Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.

23. Yakan sa sauran al'ummai su yi ƙarfi su ƙasaita,Sa'an nan ya fatattaka su, ya hallaka su.

24. Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye,Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,

25. Su yi ta lalube cikin duhu, su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.”

Karanta cikakken babi Ayu 12