Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 12:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ayuba ya amsa.

2. “Aha! Ashe, kai ne muryar jama'a,Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.

3. Amma ni ma ina da hankali gwargwado, kamar yadda kake da shi,Ban ga yadda ka fi ni ba.Kowa ya san sukan abin da ka faɗa.

4. Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu,Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi,Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.

5. Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya.Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.

6. Amma ɓarayi da marasa tsoronAllah suna zaune cikin salama,Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.

7. “Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani,Suna da abu mai yawa da za su koya maka.

8. Ka roƙi talikan da suke a duniya, da cikin teku, hikimar da suke da ita.

9. Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.

10. Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa.Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.

11. Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci,Haka nan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi.

Karanta cikakken babi Ayu 12