Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 11:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zofar ya amsa.

2. “Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu?Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai?

3. Ayuba,kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba?Kana tsammani maganganunka na ba'aZa su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?

4. Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne,Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.

5. Da ma Allah zai amsa maka,Ya yi magana gāba da kai,

6. Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa.Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam.Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.

Karanta cikakken babi Ayu 11