Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 3:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Zai yiwu mutane su rasa firgita,Idan aka busa ƙahon yaƙi abirni?Zai yiwu wata babbar masifa ta aukowa birniBa da yardar Ubangiji ba?

7. Hakika Ubangiji ba yakan aikatakome ba,Sai da sanin bayinsa annabawa.

8. Zaki ya yi ruri!Wa ba zai ji tsoro ba?Sa'ad da Ubangiji ya yi magana!Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?

9. Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”

10. Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.

11. “Saboda haka abokan gaba za sukewaye ƙasarsu,Su hallakar da kagaransu,Su washe gidajen nan nasu masudaraja.”

12. Ubangiji ya ce,“Kamar yadda makiyayi yakan ceciƙafafu biyuKo kunne ɗaya na tunkiya dagabakin zaki,Haka nan kuma kima daga cikinmutanen SamariyaWaɗanda suke zaman jin daɗi za sutsira.

13. Ku saurara yanzu,Ku yi wa zuriyar Yakubu kashedi,”In ji Ubangiji, Maɗaukaki.

14. “Ran da na hukunta mutanenIsra'ila saboda zunubansu,Zan hallakar da bagadan Betel.Za a kakkarya zankayen bagaden,Su fāɗi ƙasa.

Karanta cikakken babi Amos 3