Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 3:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.

11. “Saboda haka abokan gaba za sukewaye ƙasarsu,Su hallakar da kagaransu,Su washe gidajen nan nasu masudaraja.”

12. Ubangiji ya ce,“Kamar yadda makiyayi yakan ceciƙafafu biyuKo kunne ɗaya na tunkiya dagabakin zaki,Haka nan kuma kima daga cikinmutanen SamariyaWaɗanda suke zaman jin daɗi za sutsira.

13. Ku saurara yanzu,Ku yi wa zuriyar Yakubu kashedi,”In ji Ubangiji, Maɗaukaki.

14. “Ran da na hukunta mutanenIsra'ila saboda zunubansu,Zan hallakar da bagadan Betel.Za a kakkarya zankayen bagaden,Su fāɗi ƙasa.

Karanta cikakken babi Amos 3