Jama'ar Isra'ila da na Yahuza waɗanda suke zaune a garuruwan Yahuza, su ma sun kawo tasu zaka ta shanu, da ta tumaki, da ta abubuwan da aka keɓe aka kuma tsarkake domin Ubangiji Allahnsu, suka tara su tsibi tsibi.