Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 31:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. sa'an nan da Yehiyel, da Azaziya, da Nahat, da Asahel, da Yerimot, da Yozabad, da Eliyel, da Ismakiya, da Mahat, da Benaiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimai waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban Haikalin Allah suka naɗa.

14. Kore kuwa ɗan Imna Balawe, mai tsaron ƙofar gabas, yake lura da hadayu na yardar rai ga Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.

15. Eden, da Miniyamin, da Yeshuwa, da Shemaiya, da Amariya, da Shekaniya suna taimakonsa da zuciya ɗaya a biranen firistoci, don su rarraba wa 'yan'uwansu rabonsu, tsofaffi da yara, duka ɗaya ne, bisa ga ƙungiyoyinsu,

16. da su kuma waɗanda aka rubuta bisa ga asali, 'yan samari masu shekara uku zuwa sama, duk dai waɗanda za su shiga Haikalin Ubangiji don yin hidima, kamar yadda aka tsara, bisa ga matsayinsu yadda aka karkasa su.

17. Aka kuma rubuta firistoci bisa ga gidajen kakanninsu, na wajen Lawiyawa kuwa, tun daga mai shekara ashirin zuwa sama, bisa ga matsayinsu, ta yadda aka karkasa su.

18. Aka rubuta firistoci tare da dukan ƙananan 'ya'yansu, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, dukansu gaba ɗaya, gama da zuciya ɗaya suka tsarkake kansu.

19. Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa 'ya'yan Haruna, firist, maza kuwa, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namiji da aka rubuta na Lawiyawa, nasa rabo.

20. Haka kuwa Hezekiya ya yi a dukan Yahuza, ya aikata abin da yake daidai, da aminci, a gaban Ubangiji Allahnsa.

21. Kowane irin aiki da ya kama na hidimar Haikalin Allah, wanda yake kuma bisa ga doka da umarni, na neman Allahnsa, ya yi su da zuciya ɗaya, ya kuwa arzuta.

Karanta cikakken babi 2 Tar 31