Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 29:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Hezekiya ya ci sarauta sa'ad da yake da shekara ashirin da biyar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abaija, 'yar Zakariya.

2. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi duka.

3. A shekara ta fari ta mulkinsa, a wata na farko, sai ya buɗe ƙofofin Haikalin Ubangiji ya gyaggyara su.

4. Sai ya shigo da firistoci da Lawiyawa, ya tara su a filin da yake wajen gabas.

5. Sai ya ce musu, “Ku ji ni, ya ku Lawiyawa. Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake Haikalin Ubangiji Allah na kakanninku, ku kawar da ƙazantar da yake a Wuri Mai Tsarki.

6. Gama kakanninmu sun yi rashin aminci, sun aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnmu, sun rabu da shi sun ba da baya ga mazaunin Ubangiji.

7. Sun kuma rurrufe ƙofofin shirayi suka kashe fitilu, sun daina ƙona turare ko miƙa hadayun ƙonawa a Wuri Mai Tsarki ga Allah na Isra'ila.

8. Don haka Ubangiji ya yi fushi da Yahuza da Urushalima, ya sa suka zauna da tsoro, abin banmamaki, abin ba'a kamar yadda kuke gani da idanunku.

9. Saboda wannan an kashe kakanninmu da takobi, 'ya'yanmu mata, da 'ya'yanmu maza da matanmu, an kai su bauta.

10. “Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra'ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu.

11. 'Ya'yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.”

Karanta cikakken babi 2 Tar 29