Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 27:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ya kuma gina birane a ƙasar tuddai ta Yahuza, da kagara, da hasumiya a tuddai masu kuramu.

5. Ya yi yaƙi da Sarkin Ammonawa, ya kuwa ci nasara, har Ammonawa suka ba shi talanti ɗari na azurfa a wannan shekara, da alkama mudu dubu goma (10,000) da sha'ir mudu dubu goma (10,000). Haka Ammonawa suka yi ta biya a shekara ta biyu da ta uku.

6. Yotam ya shahara, saboda ya daidaita al'amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 27