Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 22:11-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Amma sai Yehosheba, 'yar sarki Yoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya, ta sace shi daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe su ta sa shi da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba 'yar sarki Yoram, matar Yehoyada firist, ta yi, gama ita 'yar'uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya ta kashe shi.

12. Yowash yana ɓoye a Haikalin Allah har shekara shida, a lokacin da Ataliya take mulkin ƙasar.

Karanta cikakken babi 2 Tar 22