Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 17:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Suka koyar a Yahuza, suna tare da Littafin Shari'ar Ubangiji, wato Attaura. Suka shiga ko'ina a biranen Yahuza suka koyar da jama'a.

10. Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashen da suke kewaye da Yahuza, har ba su iya fāɗa wa Yehoshafat da yaƙi ba.

11. Sai waɗansu daga cikin Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa domin haraji. Larabawa ma suka kawo masa raguna dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700), da bunsurai dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700).

12. Yehoshafat ya daɗa ƙasaita, ya giggina kagarai, da biranen ajiya a Yahuza.

13. Yana kuwa da manya manyan wuraren ajiya a biranen Yahuza.Yana kuma da gwarzayen sojoji masu yawa a Urushalima.

14. Ga jimillar sojojin bisa ga gidajen kakanninsu. Na Yahuza mai shugabannin dubu dubu, shugaba Adana yana shugabancin sojoji dubu ɗari uku (300,000) gwarzaye.

15. Mai bi masa, sai shugaba Yehohanan yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000).

16. Mai biye da Yehohanan kuma shi ne shugaba Amasiya, ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa don bauta wa Ubangiji, shi kuma yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000) gwarzaye.

17. Na Biliyaminu kuma sarkin yaƙi shi ne Eliyada, gwarzo ne, yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000), 'yan baka da garkuwa.

18. Na biye da Eliyada kuma shi ne shugaba Yehozabad wanda yake da sojoji dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) shirayayyu don gabza yaƙi.

19. Waɗannan suke yi wa sarki hidima, banda waɗanda sarki ya sa a birane masu kagara ko'ina a Yahuza.

Karanta cikakken babi 2 Tar 17