Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 17:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yehoshafat ɗansa kuwa ya gāji gadon sarautarsa, ya kahu sosai gāba da Isra'ila.

2. Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi.

3. Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat saboda ya bi halin tsohonsa da ya yi da fari, bai kuwa nemi Ba'al ba.

4. Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra'ila ba.

5. Saboda haka ne Ubangiji ya ba shi ikon riƙon wannan mulki. Yahuza duka kuwa ta kawo wa Yehoshafat haraji, ya kuwa zama riƙaƙƙen mai dukiya, wanda kuma ake girmamawa.

6. Zuciyarsa ta ƙarfafa cikin al'amuran Ubangiji. Ya kawar da masujadai, da Ashtarot daga ƙasar Yahuza.

7. A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya aika da ma'aikatansa, su Ben-hail, da Obadiya, da Zakariya, da Netanel, da kuma Mikaiya don su yi koyarwa a biranen Yahuza.

8. Tare da su kuma akwai Lawiyawa, da Shemaiya, da Netaniya, da Zabadiya, da Asahel, da Shemiramot, da Jonatan, da Adonaija, da Tobiya, da Tob-adonaija, tare da waɗannan Lawiyawa akwai firistoci, Elishama da Yehoram.

9. Suka koyar a Yahuza, suna tare da Littafin Shari'ar Ubangiji, wato Attaura. Suka shiga ko'ina a biranen Yahuza suka koyar da jama'a.

Karanta cikakken babi 2 Tar 17