Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 3:23-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sai suka ce, “Wannan jini ne, hakika sarakunan sun yi yaƙi da juna, sun karkashe juna. Bari mu tafi mu kwashi ganima!”

24. Da suka kai sansanin Isra'ilawa, sai Isra'ilawa suka tashi, suka fāɗa musu, har suka gudu. Isra'ilawa kuwa suka bi su, suna ta karkashe su,

25. suka lalatar da biranensu, a kowace kyakkyawar gona kuma, kowannensu ya jefa dutse a cikinta, har aka cika ta da duwatsu, suka kuma tattoshe kowace maɓuɓɓugar ruwa, suka sassare kyawawan itatuwa. Babban birnin Kir-hareset kaɗai ya ragu, Isra'ilawa suka kewaye shi suka fāɗa shi da yaƙi.

26. Da Sarkin Mowab ya ga yaƙin ya juya masa baya, sai ya zaɓi masu takobi ɗari bakwai ya kutsa kai a wajen ɓayar Sarkin Edom, amma suka kāsa.

27. Sai Sarkin Mowab ya kama babban ɗansa, wanda zai gāji sarautarsa, ya miƙa shi hadayar ƙonawa a kan garu. Isra'ilawa kuwa suka tsorata ko allahn abokan gāba zai cuce su, don haka suka janye, suka koma ƙasarsu.

Karanta cikakken babi 2 Sar 3