Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 22:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ya kuma ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Ya kuwa karanta wa sarki littafin.

11. Sa'ad da sarki ya ji maganar da take cikin littafin dokoki, sai ya kece tufafinsa.

12. Sa'an nan ya umarci Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikaiya, da Shafan magatakarda, da Asaya baran sarki cewa,

13. “Ku tafi ku yi tambaya ga Ubangiji saboda ni, da jama'a, da dukan mutanen Yahuza a kan maganar littafin nan da aka samo, gama Ubangiji ya yi fushi da muƙwarai saboda kakanninmu domin ba su bi maganar littafin nan ba, har da za su yi dukan abin da aka rubuta mana.”

14. Sai Hilkiya firist, da Ahikam, da Akbor, da Shafan, da Asaya suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, wato jikan Harhas, mai tsaron ɗakin da ake ajiye tufafi. A Urushalima take zaune a sabuwar unguwa. Suka kuwa yi magana da ita.

15. Sai ta ce musu, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, a faɗa wa mutumin da ya aiko ku gare ni,

16. ‘Ga shi, zan aukar da masifa a wurin nan, da a mazaunan wurin, bisa ga dukan maganar littafin nan wanda Sarkin Yahuza ya karanta,

Karanta cikakken babi 2 Sar 22