Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 21:18-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Manassa ya mutu, aka binne shi a lambun gidansa a gonar Uzza. Ɗansa Amon ya gāji gadon sarautarsa.

19. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Meshullemet, 'yar Haruz na Yotba.

20. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Manassa ya yi.

21. Ya bi halin tsohonsa duka. Ya bauta wa gumakan da tsohonsa ya bauta wa, ya kuma yi musu sujada.

22. Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai bi tafarkin Ubangiji ba.

23. Fādawansa kuwa suka ƙulla masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.

24. Amma mutanen ƙasar suka kashe waɗannan da suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar. Sai suka naɗa Yosiya ɗan sarki, ya gāji tsohonsa.

25. Sauran ayyukan da Amon ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

26. Aka binne shi a kabarinsa na gonar Uzza. Ɗansa Yosiya ya gāji sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 21