Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 2:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. suka kuma ce masa, “Yanzu fa, ga mu mu hamsin ƙarfafa. Bari mu tafi mu nemo maigidanka, mai yiwuwa ne Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi, ya jefa shi kan wani dutse, ko cikin wani kwari.”Elisha ya ce, “Kada ku tafi.”

17. Amma suka matsa masa har suka i masa, sai ya yardar musu su tafi. Su kuwa suka tafi su hamsin. Suka yi ta neman Iliya, har kwana uku, amma ba su same shi ba.

18. Sa'an nan suka komo wurinsa a Yariko. Sai ya ce musu, “Ai, dā ma na ce muku kada ku tafi.”

19. Waɗansu mutanen gari suka ce wa Elisha, “Ga shi, garin yana da kyan gani, amma ruwan ba kyau, yana sa ana yin ɓari.”

20. Elisha kuwa ya ce, “Ku kawo mini gishiri a sabuwar ƙwarya.” Su kuwa suka kawo masa,

21. sai ya tafi maɓuɓɓugar ruwa yana barbaɗa gishirin, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da wannan ruwa, ba zai ƙara sa a mutu ko a yi ɓari ba.’ ”

22. Ruwan kuwa ya gyaru bisa ga maganar Elisha, har wa yau.

23. Daga nan Elisha ya haura zuwa Betel. A hanya sai ga waɗansu samari sun fito daga cikin gari, suna yi masa eho, suna cewa, “Ka bar wurin nan, kai mai saiƙo.”

24. Elisha ya waiga, ya gan su, ya la'anta su da sunan Ubangiji. Sai waɗansu namomin jeji guda biyu suka fito daga cikin kurmi suka yayyage arba'in da biyu daga cikin samarin.

25. Daga nan Elisha ya tafi har Dutsen Karmel, sa'an nan ya koma Samariya.

Karanta cikakken babi 2 Sar 2