Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 19:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da sarki Hezekiya ya ji wannan magana, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa rigar makoki, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji.

2. Sai ya aiki Eliyakim wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da manyan firistoci, saye da tufafin makoki zuwa wurin annabi Ishaya, ɗan Amoz,

3. su ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, 'ya'ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.

Karanta cikakken babi 2 Sar 19