Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 12:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta bakwai ta sarautar Yehu, Yowash ya ci sarautar. Ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya ta Biyer-sheba.

2. Yowash kuwa ya yi abin da yake daidai ga Ubangiji dukan kwanakinsa, domin Yehoyaka, firist, ya koya masa.

3. Duk da haka ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba, mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a kan tuddan.

4. Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali,

5. sai ku karɓa daga junanku, don a gyara duk inda ake bukatar gyara a Haikalin.”

6. Amma har a shekara ta ashirin da uku ta sarautar sarki Yowash, firistocin ba su yi wani gyara a Haikalin ba.

7. Saboda haka Yowash ya kirawo Yehoyada, firist, da sauran firistoci, ya ce musu, “Me ya sa ba ku gyara Haikalin? Daga yanzu kada ku karɓi kuɗi daga wurin abokanku, sai in za ku ba da shi domin gyaran Haikalin.”

8. Firistocin kuwa suka yarda, ba za su karɓi kuɗi daga wurin jama'a ba, ba su kuwa gyara Haikalin ba.

9. Sa'an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa'an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji.

10. Sa'ad da suka gani akwai kuɗi da yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki, da babban firist suka zo, suka ƙirga kuɗin da yake a Haikalin Ubangiji suka ƙunsa shi a babbar jaka.

Karanta cikakken babi 2 Sar 12