Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 9:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dawuda ya yi tambaya, ko akwai wani da ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna wa alheri saboda Jonatan.

2. Akwai wani bara na gidan Saul, sunansa Ziba. Sai aka kirawo shi wurin sarki Dawuda. Sarki ya tambaye shi, “Kai ne Ziba?”Sai ya amsa, “Ranka ya daɗe, ni ne.”

3. Sa'an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah.Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”

4. Sai sarki ya tambaye shi, “Ina yake?”Ziba ya ce, “Yana gidan Makir, ɗan Ammiyel a Lodebar.”

5. Sarki kuwa ya aika aka zo da shi daga gidan Makir, ɗan Ammiyel, daga Lodebar.

Karanta cikakken babi 2 Sam 9