1. Bayan haka kuma sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar.
2. Sa'an nan ya ci Mowabawa da yaƙi. Ya sa su su kwanta a ƙasa sa'an nan ya riƙa auna su da igiya, kowane awo biyu ya sa a kashe su, awo na uku kuwa sai ya sa a bar su da rai. Mowabawa suka zama talakawansa, suka riƙa kawo haraji.