Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 22:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ya hau kerub, ya tashi sama,Ya yi tafiya ta fikafikan iska.

12. Ya rufe kansa da duhu,Gizagizai masu kauri cike da ruwa suna kewaye da shi,

13. Garwashi mai ci daga tsawar walƙiya a gabansa.

14. “Ubangiji ya yi tsawa daga sararin samaAka kuma ji muryar Maɗaukaki.

15. Ya harharba kibau, ya warwatsa magabtansa,Da walƙiyoyin tsawa ya sa su gudu.

16. An bayyana ƙarƙashin teku a fili,An tone tussan duniya,Lokacin da Ubangiji ya yi wa abokan gāba tsautawa,Ya yi musu ruri cikin fushi.

17. Daga Sama Ubangiji ya miƙo ya ɗauke ni,Ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.

18. Ya kuɓutar da ni daga waɗanda suke ƙina,Daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina!

Karanta cikakken babi 2 Sam 22