Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 21:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Daga can ne ya kwaso ƙasusuwan Saul da na Jonatan, suka kuma tattara ƙasusuwan waɗanda aka rataye.

14. Aka binne ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan a kabarin Kish, tsohon Saul, a Zela a ƙasar Biliyaminu. Aka aikata dukan abin da sarki ya umarta. Bayan haka Allah ya ji addu'arsu a kan ƙasar.

15. Ana nan sai Filistiyawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi. Dawuda kuwa ya gangara tare da jama'arsa, suka yi yaƙi da Filistiyawa. Dawuda kuwa ya gaji.

16. Sai Ishbi-benob, ɗaya daga cikin Refayawa, gwarzayen nan, wanda nauyin mashinsa ya yi shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma rataye da sabon takobi, ya zaci zai iya kashe Dawuda.

17. Abishai ɗan Zeruya kuwa, ya kawo wa Dawuda gudunmawa. Ya faɗa wa Bafilisten, ya kashe shi. Jama'ar Dawuda kuwa suka sa ya yi musu alkawari ba zai ƙara binsu zuwa wurin yaƙi ba. Suka ce, “Kai ne begen Isra'ila, ba mu so mu rasa ka.”

18. Bayan wannan kuma suka sāke yin yaƙi da Filistiyawa a Gab. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin gwarzayen.

19. Suka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gab, sai Elhanan, ɗan Yayir, mutumin Baitalami, ya kashe ɗan'uwan Goliyat na Gat, wanda girman gorar māshinsa ta yi kama da dirkar masaƙa.

20. An kuma yi wani yaƙi a Gat, inda aka sami wani ƙaton mutum wanda shi cindo ne, hannuwa da ƙafafu, wato yana da yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi kuma daga cikin zuriyar gwarzayen mutanen ne.

21. Sa'ad da ya nuna wa Isra'ilawa raini, Jonatan ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda, ya kashe shi.

22. Waɗannan gwarzaye huɗu sun fito daga zuriyar gwarzayen Gat ne. Dawuda da mutanensa suka kashe su.

Karanta cikakken babi 2 Sam 21