Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 21:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.”

2. (Gibeyonawa dai ba mutanen Isra'ila ba ne, su Amoriyawan da suka ragu ne, waɗanda Isra'ilawa suka rantse musu, cewa, ba za su kashe su ba. Amma Saul, saboda kishin da yake yi domin mutanen Isra'ila da Yahuza, ya nema ya kashe su duk.)

3. Dawuda kuwa ya kira Gibeyonawa ya ce musu, “Me zan yi muku, da me zan yi kafara, domin ku sa wa mutanen Ubangiji albarka?”

4. Gibeyonawa suka amsa suka ce, “Ba zancen azurfa ko zinariya yake tsakaninmu da Saul ko da gidansa ba. Ba kuma wani mutum muke so mu kashe daga cikin Isra'ila ba.”Dawuda kuma ya tambaye su ya ce, “To, me kuke so in yi muku?”

5. Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya karkashe mu, ya yi niyyar hallakar da mu, don kada mu kasance tare da Isra'ilawa ko'ina a cikin karkararsu.

6. Sai ka ba mu 'ya'yansa maza bakwai domin mu rataye su a gaban Ubangiji a Gibeya a kan dutsen Ubangiji.”Sarki kuwa ya ce, “To, zan bayar.”

7. Amma sarki ya ware Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, saboda rantsuwar da yake tsakaninsa da Jonatan, ɗan Saul.

8. Sai sarki ya sa aka kamo masa Armoni da Mefiboshet, 'ya'yan Saul waɗanda Rizfa, 'yar Aiya, ta haifa masa, da 'ya'ya maza biyar na Adriyel, ɗan Barzillai, mutumin Abelmehola, waɗanda matarsa Merab 'yar Saul ta haifa masa.

Karanta cikakken babi 2 Sam 21