Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 2:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.

12. Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon.

13. Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin.

14. Sai Abner ya ce wa Yowab, “Bari samarin su tashi su yi kokawa a gabanmu.”Yowab kuwa ya ce, “To, sai su tashi.”

15. Sai suka tashi, suka haye. Mutum goma sha biyu a madadin mutanen Biliyaminu da Ish-boshet, ɗan Saul, mutum goma sha biyu kuma a madadin mutanen Dawuda.

16. Kowa ya kama abokin kokawarsa a kā, suka soki juna a kwiɓi da takuba. Suka faɗi tare. Aka sa wa wurin suna Helkat-hazzurim, wato filin takuba, wurin yana nan a Gibeyon.

17. Yaƙin kuwa ya yi zafi a ranar. Mutanen Dawuda suka ci Abner da mutanen Isra'ila.

18. 'Ya'yan Zeruya, maza, su uku suna nan, wato Yowab, da Abishai, da Asahel. Asahel maguji ne kamar barewa.

19. Sai ya tasar wa bin Abner haiƙan, bai kauce ba.

Karanta cikakken babi 2 Sam 2