Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 13:31-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Sai sarki ya tashi ya keta rigunansa, ya kwanta a ƙasa. Dukan barorinsa kuma da suke tsaye a wurin suka kyakketa rigunansu.

32. Amma Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda, ya ce, “Ranka ya daɗe, ba fa dukan 'ya'yan sarki aka kashe ba. Amnon ne kaɗai aka kashe ta umarnin Absalom, gama ya ƙudura wannan tun daga ranar da Amnon ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.

33. Don haka, kada shugabana sarki ya damu, cewa, an kashe dukan 'ya'yan sarki, gama Amnon ne kaɗai aka kashe.”

34. Absalom kuwa ya gudu.Sa'an nan sojan da yake tsaro a wannan lokaci ya ga ɗumbun mutane suna tahowa daga hanyar Horonayim, wajen gefen dutse.

35. Sai Yonadab ya ce wa sarki, “Waɗannan 'ya'yan sarki ne yake zuwa, kamar yadda na faɗa.”

36. Yana gama magana ke nan, sai ga 'ya'yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.

37. Amma Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai, ɗan Ammihud, Sarkin Geshur. Dawuda kuwa ya yi makokin Amnon ɗansa kwana da kwanaki.

38. Absalom ya shekara uku a Geshur.

39. Sai zuciyar sarki ta koma kan Absalom, gama ya haƙura a kan Amnon da yake ya riga ya rasu.

Karanta cikakken babi 2 Sam 13