Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 11:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa'an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.”

16. Sa'ad da Yowab yake kama garin da yaƙi, sai ya sa Uriya a inda ya sani akwai jarumawan gaske.

17. Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.

18. Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin.

19-20. Ya ce wa manzo, “Bayan da ka gama faɗa wa sarki labarin yaƙin duka, idan sarki ya husata, har ya ce maka, ‘Me ya sa kuka tafi yaƙi kurkusa da garin? Ba ku sani ba za su tsaya a gefen garu daga ciki su yi harbi?

21. Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubba'al? Ba mace ce a TebEze ta jefe shi da ɗan dutsen niƙa ta kan garu daga ciki ta kashe shi ba? Me ya sa kuka tafi kusa da garu?’ Sai ka faɗa masa cewa, ‘Baranka, Uriya Bahitte, shi ma an kashe shi.’ ”

22. Manzon kuwa ya tafi ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Yowab ya ce.

23. Ya ce, “Abokan gābanmu sun sami sa'a a kanmu. Sun fito su gabza da mu a karkara, amma muka kore su zuwa cikin ƙofar garin.

24. Sai maharba suka tsaya a kan garu daga ciki suka yi ta harbin barorinka. Waɗansu daga cikin barorin sarki sun mutu. Baranka Uriya Bahitte shi ma ya matu.”

25. Dawuda ya ce wa manzon, “Je ka ka faɗa wa Yowab kada wannan abu ya dame shi, ai, takobi ba ya tarar wanda zai kashe. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku faɗa masa har ku ragargaza shi. Ka ƙarfafa Yowab.”

26. Sa'ad da matar Uriya ta ji labarin mutuwar mijinta, ta yi makoki dominsa.

27. Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.

Karanta cikakken babi 2 Sam 11