Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 1:12-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Suka yi makoki, da kuka, da azumi har maraice saboda Saul, da Jonatan ɗansa, da mutanen Ubangiji, da gidan Isra'ila domin an Karkashe su a yaƙi.

13. Dawuda ya ce wa mutumin nan da ya kawo labarin, “Daga ina ka zo?”Sai ya ce masa, “Ai, ni ɗan wani baƙo ne, Ba'amaleke.”

14. Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?”

15. Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin samarin, ya ce masa, “Ka kashe shi.” Ya dai buge shi, ya mutu.

16. Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.’ ”

17. Sai Dawuda ya raira waƙar makoki domin Saul da Jonatan, ɗansa.

Karanta cikakken babi 2 Sam 1