Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 8:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Waɗannan kuma su ne 'ya'yan Ehud, maza. Su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Geba, waɗanda aka kai su bauta a Manahat.

7. Ga sunayensu, Na'aman, da Ahaija, da Gera wanda yake shugabansu lokacin da aka kai su bauta. Shi ne kuma mahaifin Uzza da Ahihud.

8. Shaharayim kuma yana da 'ya'ya maza a ƙasar Mowab bayan da ya saki matansa biyu, wato Hushim da Ba'ara.

9. Matarsa Hodesh ta haifa masa 'ya'ya maza, su ne Yobab, da Zibiya, da Mesha, da Malkam,

Karanta cikakken babi 1 Tar 8