Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 8:36-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Allemet, da Azmawet, da Zimri. Zimri ya haifi Moza.

37. Moza ya haifi Bineya, da Refaya, da Eleyasa, da Azel.

38. Azel ya haifi 'ya'ya maza su shida, su ne Azrikam, da Bokeru, da Ismayel, da Sheyariya, da Obadiya, da Hanan.

39. 'Ya'ya maza na Esheke ɗan'uwansa su ne, Ulam, da Yewush, da Elifelet.

40. 'Ya'yan Ulam, maza, jarumawa ne sosai, 'yan baka, suna da 'ya'ya maza, da jikoki maza da yawa. Su ɗari da hamsin ne. Waɗannan duka mutanen Biliyaminu ne.

Karanta cikakken babi 1 Tar 8