Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 8:25-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. da Ifediya, da Feniyel.

26. Zuriyar Yeroham, su ne Shemsherai, da Shehariya, da Ataliya,

27. da Yawareshiya, da Eliya, da Zikri.

28. Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakanninsu a zamaninsu, waɗanda suka zauna a Urushalima.

29. Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a can. Sunan matarsa Ma'aka.

30. Abdon ne ɗansa na fari, sa'an nan Zur, da Kish, da Ba'al, da Nadab,

31. da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya,

32. da Miklot, mahaifin Shimeya. Waɗannan su ne suka zauna daura da 'yan'uwansu a Urushalima.

33. Ner shi ne mahaifin Kish, Kish kuma shi ne mahaifin Saul, Saul shi ne mahaifin Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.

34. Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika.

35. 'Ya'yan Mika, maza, su ne Fiton, da Melek, da Tareya, da Ahaz.

36. Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Allemet, da Azmawet, da Zimri. Zimri ya haifi Moza.

37. Moza ya haifi Bineya, da Refaya, da Eleyasa, da Azel.

38. Azel ya haifi 'ya'ya maza su shida, su ne Azrikam, da Bokeru, da Ismayel, da Sheyariya, da Obadiya, da Hanan.

39. 'Ya'ya maza na Esheke ɗan'uwansa su ne, Ulam, da Yewush, da Elifelet.

40. 'Ya'yan Ulam, maza, jarumawa ne sosai, 'yan baka, suna da 'ya'ya maza, da jikoki maza da yawa. Su ɗari da hamsin ne. Waɗannan duka mutanen Biliyaminu ne.

Karanta cikakken babi 1 Tar 8