Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 7:11-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Duk waɗannan 'ya'yan Yediyayel, maza ne, bisa ga shugabannin gidajen kakanninsu. Su dubu goma sha bakwai ne da ɗari biyu (17,200), jarumawa ne sosai, shiryayyu don yaƙi.

12. Shuffim da Huffim su ne 'ya'yan Iri, maza.Hushim shi ne ɗan Ahiram.

13. Naftali yana da 'ya'ya huɗu, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum. Su ne zuriya daga Bilha.

14. 'Ya'yan Manassa, maza, su ne Asriyel, wanda ƙwarƙwararsa Ba'aramiya ta haifa masa. Ta kuma haifi Makir mahaifin Gileyad.

15. Makir ya auro wa Huffim da Shuffim mata. Sunan 'yar'uwarsa Ma'aka, sunan ɗan'uwansa kuwa Zelofehad, Zelofehad yana da 'ya'ya mata kaɗai.

16. Sai Ma'aka matar Makir ta haifi ɗa, ta sa masa suna Feres, sunan ɗan'uwansa kuwa Sheres. 'Ya'yan Feres maza, su ne Ulam da Rakem.

17. Ɗan Ulam shi ne Bedan. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Gileyad ɗan Makir, jīkan Manassa.

18. 'Yar'uwarsa, Hammoleket ta haifi Ishodi, da Abiyezer, da Mala.

19. 'Ya'yan Shemida, maza, su ne Ahiyan, da Shekem, da Liki, da Aniyam.

20. 'Ya'yan Ifraimu, maza, daga tsara zuwa tsara, su ne Shutela, da Bered, da Tahat, da Eleyada, da Tahat,

21. da Zabad, da Shutela, da Ezer, da Eleyad waɗanda mutanen Gat, haifaffun ƙasar, suka kashe sa'ad da suka kai hari don su kwashe dabbobinsu.

22. Sai mahaifinsu, Ifraimu, ya yi ta makoki kwanaki da yawa. 'Yan'uwansu kuwa suka zo don su yi masa ta'aziyya.

23. Sa'an nan ya shiga wurin matarsa, ta kuwa sami juna biyu, ta haifi ɗa, ya raɗa masa suna Beriya saboda masifar da ta auko wa gidansa.

24. 'Yarsa kuma ita ce Sheyera, wadda ta gina garin Bet-horon na kwari da na tudu, ta kuma gina Uzzen-sheyera.

25. Waɗansu zuriyarsa bi da bi, su ne Refa, da Reshe, da Tela, da Tahan,

Karanta cikakken babi 1 Tar 7