Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 6:68-81 Littafi Mai Tsarki (HAU)

68. da Yokmeyam duk da makiyayarta, da Bet-horon duk da makiyayarta,

69. da Ayalon duk da makiyayarta, da Gatrimmon duk da makiyayarta.

70. Daga cikin rabin kabilar Manassa kuma an ba su Ta'anak duk da makiyayarta, da Bileyam duk da makiyayarta. An ba da waÉ—annan ga sauran iyalai na 'ya'yan Kohat, maza.

71. Daga na rabin kabilar Manassa na gabas, an ba 'ya'yan Gershon, maza, Golan ta Bashan tare da makiyayarta, da Ashtarot duk da makiyayarta.

72. Daga na kabilar Issaka kuma an ba su Kishiyon duk da makiyayarta, da Daberat duk da makiyayarta,

73. da Ramot duk da makiyayarta, da Enganin duk da makiyayarta.

74. Daga cikin kabilar Ashiru kuma an ba da Mishal duk da makiyayarta, da Abdon duk da makiyayarta,

75. da Helkat duk da makiyayarta, da Rehob duk da makiyayarta.

76. Daga na kabilar Naftali kuma an ba da Kedesh ta Galili duk da makiyayarta, da Hammon duk da makiyayarta, da Kartan duk da makiyayarta.

77. Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato 'ya'yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.

78. Daga na kabilar Ra'ubainu a hayin Urdun a Yariko, wato gabashin Urdun, an ba da Bezer ta cikin jeji duk da makiyayarta, da Yahaza duk da makiyayarta,

79. da Kedemot duk da makiyayarta, da Mefayat duk da makiyayarta.

80. Daga na kabilar Gad kuma an ba da Ramot ta Gileyad duk da makiyayarta, da Mahanayim duk da makiyayarta,

81. da Heshbon duk da makiyayarta, da Yazar duk da makiyayarta.

Karanta cikakken babi 1 Tar 6