Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 3:5-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba 'yar Ammiyel ta haifa masa.

6. Yana da waɗansu 'ya'ya kuma, su ne Ibhar, da Elishuwa da Elifelet,

7. da Noga, da Nefeg, da Yafiya,

8. da Elishama, da Eliyada, da kuma Elifelet, su tara ke nan.

9. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Dawuda, maza, banda 'ya'yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce 'yar'uwarsu.

10. Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat,

11. da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,

12. da Amaziya, da Azariya, da Yotam,

13. da Ahaz, da Hezekiya da Manassa,

14. da Amon, da Yosiya.

15. 'Ya'yan Yosiya, maza, su ne Yohenan ɗan farinsa, na biyu shi ne Eliyakim, na uku shi ne Zadakiya, na huɗu shi ne Yehowahaz,

16. Eliyakim yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Yekoniya, da Zadakiya.

17. 'Ya'yan Yekoniya wanda aka kama, su ne Sheyaltiyel,

18. da Malkiram, da Fedaiya, da Shenazzar, da Yekamiya, da Hoshama, da Nedabiya.

19. Fedaiya yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Zarubabel da Shimai. 'Ya'yan Zarubabel, maza, su ne Meshullam, da Hananiya, da Shelomit 'yar'uwarsu,

20. da Hashuba, da Ohel, da Berikiya, da Hasadiya, da Yushab-hesed, su biyar ke nan.

21. 'Ya'yan Hananiya, maza, su ne Felatiya, da Yeshaya, da 'ya'yan Refaya, maza, da 'ya'yan Arnan, maza, da 'ya'yan Obadiya, maza, da 'ya'yan Shekaniya, maza.

22. Ɗan Shekaniya shi ne Shemaiya. 'Ya'yan Shemaiya, maza, su ne Hattush, da Igal, da Bariya da Neyariya, da Shafat, su shida ke nan.

23. 'Ya'yan Neyariya, maza, su ne Eliyehoyenai, da Hezekiya, da Azrikam, su uku ne nan.

24. 'Ya'yan Eliyehoyenai, maza, su ne Hodawiya, da Eliyashib, da Felaya, da Akkub, da Yohenan, da Dalaya, da Anani, su bakwai ke nan.

Karanta cikakken babi 1 Tar 3