Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 25:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Na wajen Heman, su ne 'ya'yan Heman, maza, wato Bukkiya, da Mattaniya, da Uzziyel, da Shebuwel, da Yerimot, da Hananiya, da Hanani, da Eliyata, da Giddalti, da Romamti-yezer, da Yoshbekasha, da Malloti, da Hotir, da Mahaziyot.

5. Allah ya ba Heman, wato annabin sarki, 'ya'ya maza su goma sha huɗu, da 'ya'ya mata su uku, kamar yadda ya yi alkawari, domin ya ba Heman iko.

6. Dukansu tsohonsu ne yake bi da su da raira waƙoƙi, da kaɗa kuge, da molaye da garayu, cikin Haikalin Ubangiji, domin yin sujada. Asaf, da Yedutun, da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki.

7. Jimillar horarrun mawaƙa don raira waƙa ga Ubangiji, su da 'yan'uwansu, duka waɗanda suke ƙwararru, su ɗari biyu da tamanin da takwas ne.

Karanta cikakken babi 1 Tar 25