Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 23:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Dawuda ya tsufa, yana da shekaru da yawa, sai ya naɗa ɗansa Sulemanu ya zama Sarkin Isra'ila.

2. Dawuda kuwa ya tattara dukan shugabannin Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa.

3. Aka ƙidaya Lawiyawa maza tun daga mai shekara talatin har sama, jimillarsu dubu talatin da dubu takwas (38,000).

4. Sai Dawuda ya ce dubu ashirin da dubu huɗu (24,000) daga cikinsu za su yi hidimar Haikalin Ubangiji, dubu shida (6,000) kuma su zama manyan ma'aikata da alƙalai,

5. dubu huɗu (4,000) su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu (4,000) kuma za su zama masu raira yabbai ga Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda ya yi.

Karanta cikakken babi 1 Tar 23