Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 20:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da bazara, lokacin da sarakuna sukan fita su yi yaƙi, sai Yowab ya tafi da sojoji suka lalatar da ƙasar Ammonawa. Suka tafi, suka kewaye Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima. Yowab ya bugi Rabba ya yi nasara da ita.

2. Sai Dawuda ya ciro kambi daga kan sarkinsu, sai ya iske nauyinsa talanti ɗaya na zinariya ne, akwai kuma duwatsu masu daraja a cikinsa. Dawuda ya sa kambin a kansa. Ya kwaso ganima da yawa a birnin.

Karanta cikakken babi 1 Tar 20