Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 19:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab tare da dukan sojoji, ƙarfafan mutane.

9. Sai Ammonawa suka fito suka jā dāga a ƙofar birninsu. Sarakunan da suka zo suka ware suka zauna a saura.

10. Da Yowab ya ga an kafa masa yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu jarumawa na gaske a Isra'ila, ya sa su su kara da Suriyawa.

11. Sa'an nan ya sa sauran sojoji a hannun Abishai ɗan'uwansa. Suka jā dāgar yaƙi da Ammonawa.

12. Yowab ya ce wa Abishai, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, to, sai ka taimake ni, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinka, to, sai in taimake ka.

13. Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama'armu da biranen Allahnmu. Bari Ubangiji ya yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”

14. Yowab da jama'ar da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Suriyawa, sai Suriyawa suka gudu daga gabansu.

15. Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai, ɗan'uwan Yowab, suka shiga birni. Sa'an nan Yowab ya komo Urushalima.

16. Da Suriyawa suka ga Isra'ilawa sun ci su da yaƙi sai suka aiki manzanni suka kira Suriyawa waɗanda suke hayin kogi. Shobak shugaban sojojin Hadadezer ne yake shugabantarsu.

17. Sa'ad da aka faɗa wa Dawuda, sai ya tattara Isra'ilawa duka ya haye Urdun, ya zo wurinsu, ya jā dāga don ya yi yaƙi da su. Aka fara gabza yaƙi,

18. sai Suriyawa suka gudu a gaban Isra'ilawa, Dawuda ya karkashe Suriyawa, mutum dubu bakwai (7,000) masu karusai, da sojojin ƙasa dubu arba'in (40,000). Ya kuma kashe Shobak shugaban sojojin.

Karanta cikakken babi 1 Tar 19