Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 14:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.

8. Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka, sai dukan Filistiyawa suka haura, suna neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya fita domin ya yi yaƙi da su.

9. Filistiyawa suka iso kwarin Refayawa suka fara fatali da shi.

10. Sai Dawuda ya roƙi Allah, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”Ubangiji kuwa ya amsa masa, ya ce, “Ka haura, gama zan bashe su a hannunka.”

11. Sai suka haura zuwa Ba'al-ferazim, Dawuda kuwa ya ci su da yaƙi a wurin. Sai ya ce, “Allah ya raraki maƙiyana ta hannuna, kamar yadda ruwa yakan rarake ƙasa.” Don haka aka sa wa wurin suna Ba'al-ferazim.

Karanta cikakken babi 1 Tar 14