Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 11:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan Isra'ilawa kuwa suka taru wurin Dawuda a Hebron, suka ce masa, “Mu ɗaya ne da kai.

2. Ko dā can lokacin da Saul yake sarauta, kai ne kake yi wa Isra'ilawa jagora zuwa yaƙi da komowa. Ubangiji Allahnka kuwa ya ce maka, ‘Za ka yi kiwon jama'ata, wato Isra'ilawa, ka kuma shugabance su.’ ”

3. Sai dattawan Isra'ilawa suka zo wurin sarki Dawuda a Hebron. Dawuda kuwa ya yi alkawari da su a Hebron a gaban Ubangiji, ake kuwa naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila bisa ga faɗar Ubangiji ta bakin Sama'ila.

4. Sarki Dawuda kuwa, tare da dukan Isra'ilawa, suka tafi Urushalima, wato Yebus inda Yebusiyawa suke zaune.

5. Sai mazaunan Yebus, suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka Dawuda ya ci Sihiyona, gari mai kagara, wato birnin Dawuda ke nan.

6. Sai Dawuda ya ce, “Duk wanda ya ci Yebusiyawa da fari shi ne zai zama babban shugaban sojoji.” Yowab ɗan Zeruya ne ya fara tafiya, domin wannan aka maishe shi shugaba.

7. Sa'an nan Dawuda ya zauna a kagara, don haka aka kira birnin, birnin Dawuda.

8. Sai ya rutsa birnin da gini tun daga Millo. Yowab kuma ya gyaggyara sauran birnin.

9. Dawuda ya yi ta ƙasaita gaba gaba saboda Ubangiji Mai Runduna yana tare da shi.

10. Waɗannan su ne shugabanni, wato manyan jarumawan Dawuda waɗanda suka goyi bayansa sosai a mulkinsa, tare da dukan Isra'ilawa waɗanda suka naɗa shi sarki bisa ga maganar Ubangiji a kan Isra'ilawa.

11. Wannan shi ne labarin manyan jarumawan Dawuda. Yashobeyam ɗan Bahakmone shi ne shugaban jarumawa talatin. Ya karkashe mutum ɗari uku da māshinsa baki ɗaya.

12. Na biye da shi shi ne Ele'azara ɗan Dodo, Ba'ahohiye, wanda yake ɗaya daga cikin manyan jarumawan nan uku.

13. Yana tare da Dawuda a Efes-dammin sa'ad da Filistiyawa suka taru wuri ɗaya don su yi yaƙi. Akwai wata gonar sha'ir a wurin, sai jama'a suka gudu daga gaban Filistiyawa.

14. Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha'ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya cece su, ya ba su babbar nasara.

15. Wata rana sai uku daga cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara zuwa dutsen Dawuda, a kogon Adullam, sa'ad da rundunar sojojin Filistiyawa suka kafa sansani a kwarin Refayawa.

Karanta cikakken babi 1 Tar 11