Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 1:38-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. 'Ya'yan Seyir, maza kuma, su ne Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, da Dishon, da Ezer, da kuma Dishan.

39. 'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori, da Hemam. Timna ce 'yar'uwar Lotan.

40. 'Ya'yan Shobal, maza, su ne Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam.'Ya'yan Zibeyon, maza su ne Aiya da Ana.

41. Dishon shi ne ɗan Ana. 'Ya'yan Dishon, maza kuwa, su ne Hemdan, da Eshban, da Yitran, da Keran.

42. 'Ya'yan Ezer, maza, su ne Bilhan, da Zayawan, da Akan. 'Ya'yan Dishan, maza, su ne Uz da Aran.

43-50. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom kafin wani Sarkin Isra'ila ya ci sarauta.Bela ɗan Beyor, sunan birninsa kuwa DinhabaYobab ɗan Zera na BozaraHusham na ƙasar TemanHadad ɗan Bedad na Awit, wanda ya kori Madayanawa a filin MowabSamla na MasrekShawul na Rehobot wadda take bakin Kogin YufiretisBa'al-hanan ɗan AkborHadad na Fau, sunan matarsa kuma Mehetabel 'yar Matred, wato jikar Mezahab

51. Hadad kuwa ya rasu. Sarakunan Edom su ne Timna, da Alwa, da Yetet,

52. da Oholibama, da Ila, da Finon,

Karanta cikakken babi 1 Tar 1